
Mai Martaba Sarkin Lafian bare bari
Hon. Justice Dr. Sidi Bage Muhammad I CFR. Jsc Rtd.
Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Nasarawa.
Ya karbi bakoncin tawagar Kungiyar miyetti Allah kautal Hore, reshen Jihar Nasarawa,
A karkashin Jagorancin sabon Shugaban kungiyar na Riko, Alhaji Akajo Abubakar Gyara.
Alhaji Akajo A. gyara, yace sun ziyarci Mai Martaba Sarkin Lafian ne, domin gaisuwan girmamawa,
Sa’annan ya tabbatar wa Mai Martaba Sarkin Lafian bare bari, da cewa Kungiyar miyetti Allah kautal Hore, zata gudanar da cigba da aiyukanta cikin adalci da gaskiya da Amana.
A jawabin sa Mai Martaba Sarkin Lafian bare bari,
Ya bayyana farin cikinsa, Daggane da Wannan ziyaran tasu.
Daga bisani Mai Martaba Sarkin Lafia, yayi masu kyautar Goro irin ta al’ada.
Sa’annan yasanya wa Kungiyar al’barka.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko abknaisa100@yahoo.com

