By Ikramatu Sulaiman
Alhaji Aminu Ado Bayero yace kungiyar tana da matukar muhimmaci bisa la’akari da yadda take kokarin wayar da kan matasa akan tarbiya da dogaro da Kai.
Sarkin ya bayyana Hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar Arewa Pirth Initiative karkashin shugaban kungiyar Alhaji Aminu Adam a fadarsa.
Yace yanayin da ake ciki a Jiha da Kasa ya zama wajibi a samu wasu daga cikin al’uma hazikai su fi bijiro da abubuwan da zasu taimaka Domin rage radadin rayuwa da Kuma ayyukan yi.
Mai Martaba Sarkin Yaja hankalinsu da cewa kullum tunaninsu ya dunga kasancewa ta yaya zasu taimaki al’uma musamman matasa.
Yace dole sai sun jajirce akan wannan babban aiki da suka dakko kasancewa zasu fuskanci kalubale daban daban.
Mai Martaba Sarkin ya kara da cewa wasu daga cikin matslolin da ake samu a Jihar Kano suna zuwa ne daga wasu daga cikin jihohin dake makwabtaka da Jihar Kano
Sarki Bayero ya basu tabbacin hadin Kai da goyon bayan masarautar Kano Domin bunkasar aikin da suka dakko tareda bukatar su fadada aikin nasu Zuwa sauran jihohin arewacin kasar Nan.
Tunda farko Shugaban Kungiyar Alhaji Aminu yace sunje fadar ne domin ziyarar ban girma tareda da neman sanya albarka ga Kungiyar da Kuma neman shawarwari da gudunmawa daga Mai Martaba Sarki.
Sa Hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada labarai na Mai Martaba Sarki Kano ALHAJI Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL.
26/08/2025


