
Sabon Hakimin Rano ya bukaci hadin kan kowa don samar da ci gaba a yankin da jiha da kasa baki daya.
Dan Makwayon Rano, hakimin Rano, Alhaji Bala Garba ya nemi hadin kan ne Jim kadan da karbar aiki a matsayin wanda majalisar masarautar Rano bisa jagorancin mai martaba Sarkin Rano Dokta Muhammad Isah Umaru autan Bawo na 19 ta na da.
Wannan na cikin sanarwar manema labarai da jami’in shiyar yada labarai na shiyar Rano Abdullahi Musa Gyadi Gyadi ya rabawa manema labarai jim kadan bayan Madakin Rano, Alhaji Adda’u Isah Rano ya gabatar da shi ga majalisar karamar hukumar da duk Dagatai da masu unguwanni da sauran al’umar yankin a dakin taron karamar hukumar ta Rano a sakatariyar yankin.
Sabon Hakimin ya kuma ce zai yi iya kokarin sa wajen bada hadin kai don bunkasar yankin da masarautar ta Rano.
Ya kuma godewa duk wadanda suka taimaka don tabbatar da nasarar nada shi a matsayin hakimi.
Da ya ke jawabi Wazirin Rano, Alhaji Kabiru Sani Rano ya gargadi sabon Hakimin dama duk mai rike da shugabanci da ya zama mai adalci ga duk wanda ya ke shugabanta domin Allah zai tambaye shi yadda ya aiwatar da jagorancin a lahira.
Shugaban karamar hukumar Rano, Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano, yace majalisar karamar hukumar za ta yi aiki tare da sabon Hakimin kuma Dan Makwayon Rano, Alhaji Bala Garba musamman wajen kara samun tsaro lafiyar al’uma da dukiyoyin su.
Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano ya yi amfani da taron wajen kira ga Dagatai da masu unguwanni da dama duk al’umar yankin da su kara taimakawa wajen sanar da masu ruwa da tsaki a fannin tsaro duk lokacin da aka ga wata bakuwar fuska wadda ba su amince da ita ba a fadin karamar hukumar.
Daga nan sai ya godewa masarautar Rano bisa jagorancin mai martaba Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isah Umaru autan Bawo na 19 bisa nada Alhaji Bala Garba a matsayin Dan Makwayon Rano hakimin Rano.
Tun da farko sai da Madakin Rano Alhaji Adda’u Isah Rano ya godewa majalisar masarautar Rano da karamar hukumar da Dagatai da masu unguwanni da limamai dama al’umar yankin bisa hadin kan da suka ba shi a lokacin da ya rike wakilin sarki a yankin kafin a nada sabon Hakimin inda ya yi fatan za’a rubanya hadin kan da aka ba shi ga sabon Hakimin.
Sa hannu
Abdullahi Musa Gyadi Gyadi jami’in yada labarai na shiyar Rano

