
NNPP ta bukaci Majalisar wakilai ta sauya Ali Madaki daga mukamin mataimakin shugaban marasa rinjaye
Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta bukaci shugabannin majalisar Wakilai ta Tarayya da su sauya mataimakin shugaban marasa rinaye, Aliyu Sani Madaki, bisa zargin aikata ayyukan da suka saba da manufofin jam’iyya.
Jam’iyyar ta zargi Madaki, wanda ke wakiltar mazabar Dala ta Tarayya a jihar Kano, da karya kundin tsarin mulkin NNPP bayan an gan shi kwanan nan yana halartar taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar Dala tare da manyan jiga-jigan jam’iyyar.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na NNPP a jihar, Injiniya Ibrahim Karaye, ya fitar a ranar Laraba, jam’iyyar ta bayyana cewa matakin da dan majalisar ya dauka ba abin karba ba ne, tana mai cewa bai yi murabus daga NNPP a hukumance ba, kuma bai sanar da sauya shekarsa zuwa wata jam’iyya ba.
“Jam’iyyar na bukatar shugabancin Majalisar Tarayya ya maye gurbin Hon. Madaki da wani dan NNPP mai cikakken biyayya domin kare muradun marasa rinaye a Majalisar Tarayya da kuma dakile yunkurin APC na kafa kasa mai jam’iyya daya,” in ji Karaye.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto, Hon. Madaki bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen da kuma bukatar da jam’iyyarsa ta gabatar ba.

