Close Menu
ABKNEWS 24
  • Home
  • Business
  • Entertainment
  • Features
  • News
  • Politics
  • Security
  • Sports
  • More
    • Agriculture
    • Climate
    • Tech
    • Write Up
    • Video
  • HAUSA
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Labarai
    • Lafiya
    • Nishadi
    • Siyasa
    • Tsaro
    • Wasanni
Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
Facebook X (Twitter) Instagram
ABKNEWS 24ABKNEWS 24
Subscribe
  • Home
  • Business

    KNSG Collaborates with Zirconex for Establishment of Standard Mining Laboratory

    August 28, 2025

    SOLLONG – A NEW PHONE YOU WILL BUY WILL GET YOUR MONEY BACK AND CONTINUE TO EARN MONEY IN IT FOR A YEAR

    August 26, 2025

    SOLLONG – SABUWAR WAYAR HANNU DA ZAKA SAYA TA MAYAR MAKA DA KUDIN KA KUMA KA CIGABA DA SAMUN KUDI A CIKINTA HAR TSAWON SHEKARA DAYA

    August 26, 2025

    USSD Deductions Under Fire: Why Failed Transactions Still Attract ₦6.98 Charges

    August 21, 2025

    QNET Warns Fraudsters, Backs Ogun Gov’t Over Crackdown

    October 12, 2024
  • Entertainment

    From novels to blockbusters: Nollywood’s next frontier

    October 14, 2024

    Prioritise having kids over marriage for career success – Laide Bakare advices ladies

    October 10, 2024

    Qausain TV appoints Adam A. Zango as Director-General

    October 8, 2024

    Patrick Doyle Criticises Davido’s Attire During Visit To Olu Of Warri

    October 7, 2024

    British fencer Akinyosoye switches allegiance to Nigeria

    October 7, 2024
  • Features

    Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk Umar ya nada Sheikh Abdulkadir Jiyali a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa.

    July 23, 2026

    KEYAMO, MUSAWA CONFIRMED AS SPEAKERS AT 9TH NATIONAL TOURISM TRANSPORTATION SUMMIT & EXPO 2026: By Ado Salisu 

    July 23, 2026

    NSSF President Joseph elected ISF Africa continental president.

    July 23, 2026

    Defamation Against DSP Barau, Institutional: By Abba Anwar

    July 23, 2026

    CHANGE OF NAME: I formally known and called as ABDUL SHEHU YUSUF, now wish to be called and addressed as ABDUL SHEHU YUSIF. Former documents remain valid. General public to take note.

    July 23, 2026
  • News

    KEYAMO, MUSAWA CONFIRMED AS SPEAKERS AT 9TH NATIONAL TOURISM TRANSPORTATION SUMMIT & EXPO 2026: By Ado Salisu 

    July 23, 2026

    CHANGE OF NAME: I formally known and called as ABDUL SHEHU YUSUF, now wish to be called and addressed as ABDUL SHEHU YUSIF. Former documents remain valid. General public to take note.

    July 23, 2026

    Showcase What You Will Do Not Baseless Opposition…Tinubu Projects In The North Are Traceable, Kwankwaso.

    July 22, 2026

    Allegations of Political Interference Trail Investigation into Death of Kano Man.

    July 21, 2026

    Controversy Deepens as Senator Barau Mounts Intense Pressure on Police Following the Death of an Alleged Notorious Killer.

    July 21, 2026
  • Politics

    2027: Jamilu’s Victory, the pathway to progress of Gombe citizens

    July 15, 2026

    ADC Shahuci Ward Reaffirms Expulsion of Hajiya Naja’atu Muhammad, Rejects Claims on Kano Party Structure.

    July 12, 2026

    Tinubu’s Picking Of Shettima: Final Onslaught On The North..The Region Has Been Gotten, Musa Illiyasu Kwankwaso.

    July 11, 2026

    Niger Delta group backs President Tinubu for 2027.

    July 9, 2026

    Da Dumi Dumi: Babbar Kotun Tarayya Ta Tabbatar da Jagorancin Mark a ADC, Ta Kuma ci Tarar Abejide.

    July 2, 2026
  • Security

    THE SAFE RESCUE OF THE ABDUCTED SCHOOL CHILDREN AND THEIR TEACHERS IN OYO STATE IS A VICTORY FOR NIGERIA. WE MUST NEVER SURRENDER OUR NATION TO TERROR – DAYO ISRAEL .

    July 11, 2026

    Police not responsible for delay in establishment of state police — IGP.

    June 24, 2026

    Military rescues ex-defence spokesperson Rabe’s wife from bandits.

    June 15, 2026

    NSCDC Kano Command Dismisses Five (5) Volunteer Personnel for Unethical Conduct and Indiscipline.

    June 2, 2026

    CP Balarabe Sule rtd, expressed his happiness over the way stakeholders in Kano have come together to bring about lasting peace in the State.

    May 17, 2026
  • Sports

    NSSF President Joseph elected ISF Africa continental president.

    July 23, 2026

    Aghazu confident as Team Nigeria heads to Glasgow with medal-hungry athletics squad.

    July 23, 2026

    Oyo FA, Pillar of Sports in Partnership to Organize a Capacity Building Seminar for Football Coaches

    July 23, 2026

    Inter- Union Soccer Tourney: Pro-Chancellor tasks Northwest University athletes on NUGA Games: By Ado Salisu 

    July 21, 2026

    Team Nigeria Embarks on Final Journey from Aberdeen to Glasgow for 2026 Commonwealth Games: By Ado Salisu

    July 20, 2026
  • More
    1. Agriculture
    2. Climate
    3. Tech
    4. Write Up
    5. Video
    6. View All

    HJRBDA, Bichi and 3rd Anniversary of Tinubu’s Renewed Hope Agenda on Food Security.

    June 12, 2026

    Kano Govt Intervenes After ‘The Historica Nigeria’ Exposes Alleged Tree Felling at ARTV.

    June 7, 2026

    Agriculture: Nigeria, Vietnam Sign Strategic Pact to Boost Cashew Trade, Technology Exchange

    November 8, 2025

    Gwamnati ta fara shirin tabbatar da ƙananan manoma sun amfana da sabbin taraktocin Belarus.

    October 29, 2025

    NiMet Predicts Three-day Thunderstorm, Downpour Nationwide

    October 14, 2024

    The Sad Story Of Flooding In Niger State

    October 9, 2024

    Flood: Yobe Govt approves over N1.4bn for 25, 500 victims

    October 8, 2024

    Climate Change: Fishers Raise Alarm Over Insecurity On Seafood

    October 3, 2024

    SOLLONG – GET A SOLLONG BLOCKCHAIN DEVICE PHONE TODAY AND EARN IN USDT FOR ONE YEAR.

    August 28, 2025

    Partnership with JICA has put Nigeria’s startup ecosystem in global map -DG NITDA

    October 14, 2024

    EVENTS FOR THE WEEK 14TH TO 20TH OCTOBER, 2024. – Centre for Information Technology and Development

    October 14, 2024

    INVITATION TO APPLY: Sustainable Enterprise Challenge Project in Kano State Phase 2 – Centre for Information Technology and Development

    October 12, 2024

    Defamation Against DSP Barau, Institutional: By Abba Anwar

    July 23, 2026

    From Enlightenment to Eclipse: Nigeria’s Democracy in an Age of Shadows: By Abbati Bako,psc,bsis,UK Alumnus

    July 19, 2026

    REBUILDING PUBLIC TRUST IN LEADERSHIP: THE NASIR IDRIS EXAMPLE IN KEBBI STATE: By Ibrahim A Jombali

    July 17, 2026

    Abdulaziz, the Arewa Media Summit, and Tinubu’s Renewed Hope Agenda – By Shehu Mustapha Chaji.

    July 12, 2026

    THE DANGER OF LEADLESS SOCIETIES AND THE NEED FOR RESPONSIBLE DEMOCRACY.

    May 16, 2026

    Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk Umar ya nada Sheikh Abdulkadir Jiyali a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa.

    July 23, 2026

    KEYAMO, MUSAWA CONFIRMED AS SPEAKERS AT 9TH NATIONAL TOURISM TRANSPORTATION SUMMIT & EXPO 2026: By Ado Salisu 

    July 23, 2026

    NSSF President Joseph elected ISF Africa continental president.

    July 23, 2026

    Defamation Against DSP Barau, Institutional: By Abba Anwar

    July 23, 2026
  • HAUSA
    1. Ilimi
    2. Kasuwanci
    3. Labarai
    4. Lafiya
    5. Nishadi
    6. Siyasa
    7. Tsaro
    8. Wasanni
    9. View All

    Zaku iya tsayuwar Arfat a gidajen ku kamar yadda yazo a Hadisin Manzon Allah S.A.W – Imam Khalifa Sheikh Yusuf Ahmad Gabari

    May 24, 2026

    Alhassan Ado Doguwa ya bayyana ilimi a matsayin Kashi bayan cigaban Kowace Al’umma

    May 12, 2026

    Kwadaye da fushi nadaga cikin abubuwan dasuke jefa mutane cikin halaka. Farfesa Aminu Isma’il Sagagi.

    February 14, 2026

    Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu tace laifi ne dalibi ya boye matakin karatun da yake.

    February 8, 2026

    Mummunar Gobarar Kasuwar Singa: Anyi Asarar Biliyoyin Kudi Yayin da Gobarar ta Kone Shaguna sama da 1,000 ana gab da Shiga watan Ramadan.

    February 15, 2026

    Ramadan 2026: Farashin Zobo, Tsamiya, da Kayan Kamshi Ya Yi Tashi a Kasuwannin Kano.

    February 11, 2026

    Gobara ta tashi tareda Kone wasu Shaguna a Kasuwar Singa dake Kano a Najeriya

    November 10, 2025

    ’Yan Bindiga Sun Sace Mata 5 Ciki Har Da Masu Shayarwa A Kano Najeriya .

    November 10, 2025

    Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk Umar ya nada Sheikh Abdulkadir Jiyali a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa.

    July 23, 2026

    Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa ya kudurin gaggawa ga Majalisar Wakilai ta Kasa domin ta Sahale a sake Gina Gadojin Yankin Yaryasa dake Karamar Hukumar Tudun Wada: Auwalu Ali Sufi

    July 10, 2026

    Jam’iyyar ADC a Kano tayi Watsi Da Kwamitin Riko na Naja’atu Muhammed, Ta Kuma Bayyana shi a Matsayin Haramtacce ne.

    July 7, 2026

    ADC ta rusa shugabancin jam’iyyar na Kano tare da kafa kwamitin riƙo.

    July 6, 2026

    Ana neman al’umar Annabi SAW su taimaka domin ceto rayuwar Hajiya Khadija da Sayen Magani. Domin karin bayani 08065164420 – 08031824749

    June 30, 2026

    Shugaba Tinubu ya sake bada Umarnin a Kara Mutum 20,000 Domin Daukar su aikin “Yan Sanda Kari akan 30,000 – Hon. Aliyu Wakilai Boya

    December 3, 2025

    Gwamnatin Tarayya zata karbi Asibitin Kansa da Gwamnatin Ganduje ta gina domin Mayar dashi karkashin kulawar AKTH – Hon. Kabiru Abubakar (Abba Bichi)

    November 23, 2025

    Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Shan Inna

    October 30, 2025

    Shin Yaya kuke Kallon Sabon Shirin Film din “KADDARA” ko zai iya disashe farin jinin Shirin “LABARINA”???

    December 11, 2025

    Dawowar Jarumar Kanywood Nafisa Abdullahi Nigeria domin fara daukar Shirin “KADDARA”

    December 11, 2025

    Za’a Daura Auren Jaafar Muhammad Kabiru da Ruqayya Abubakar sai Kuma Nafisa Muhammad Kabiru da Zubairu Umar Ibrahim (Malan)

    October 27, 2025

    MAULUD: SHAHARARREN MAWAKIN NAN JAMILU JADDA GARKO YA SAKI SABUWAR WAKARSA MAI TAKEN “ANNABIN RAHAMA” A YAU JUMA’A

    September 12, 2025

    Halacci Gadon Bacci: Daga Hajiya Fatima Abdullahi Dala, APC Women leader Kano.

    July 10, 2026

    Jam’iyyar mu ba wata ƙungiya ce ta mutum daya ba – NDC.

    June 8, 2026

    “Kai ma ka taba zama yaro na a siyasa” — Ganduje ya mayar wa Kwankwaso martani

    May 29, 2026

    Matashin Dan Siyasa Hon. Musa Sani Indabo ya Mika Form din Takararsa na neman zama Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Wudil/Garko a NDC.

    May 19, 2026

    Wasu ‘Yan Bindiga Sun Yi Fashin Ragunan Layya A Kano.

    May 21, 2026

    DSS ta kama wata mata a Kano da ke safarar alburusai ga ƴan ta’adda a Katsina.

    April 2, 2026

    Rundunar yan sanda tace ta dakile harin lakurawa a jihar kebbi

    February 8, 2026

    Gwamnatin jihar Kogi ta rufe kasuwanni da tashoshin mota saboda matsalar tsaro.

    February 8, 2026

    Jami’ar bayero ta lashe gasar kwallon kwando ta jami’o’in yankin Arewa maso Yamma 

    February 8, 2026

    Ahmad Musa ya yi ritaya daga Super Eagles bayan shekaru 15 yana buga kwallo.

    December 17, 2025

    Ahmad Musa ya yi ritaya daga Super Eagles bayan shekaru 15 yana buga kwallo.

    December 17, 2025

    Yaya kuke ganin karawar da Super Eagle ta Nigeria zasuyi da Kasar Congo a yau lahadi domin samun damar shiga gasar cin kofin Duniya???

    November 16, 2025

    Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk Umar ya nada Sheikh Abdulkadir Jiyali a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa.

    July 23, 2026

    Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa ya kudurin gaggawa ga Majalisar Wakilai ta Kasa domin ta Sahale a sake Gina Gadojin Yankin Yaryasa dake Karamar Hukumar Tudun Wada: Auwalu Ali Sufi

    July 10, 2026

    Halacci Gadon Bacci: Daga Hajiya Fatima Abdullahi Dala, APC Women leader Kano.

    July 10, 2026

    Jam’iyyar ADC a Kano tayi Watsi Da Kwamitin Riko na Naja’atu Muhammed, Ta Kuma Bayyana shi a Matsayin Haramtacce ne.

    July 7, 2026
ABKNEWS 24
Home » Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Kasar Nan

Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Kasar Nan

By ABK NEWSNovember 19, 2025 Siyasa 7 Mins Read
Share
Facebook Twitter Email Telegram WhatsApp

 

Screenshot 20251119 125824

:Daga Abba Anwar

Wani babban abin lura game da rayuwar siyasar mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa, Sanata Barau Jibrin CFR, shine, yadda wasu dake masa kallon su sa’o’insa ne a siyasa, alhali kuwa karansu ko kadan bai kai tsaiko ba.

Shi dai tun ma fa a zamanin Jamhuriya ta biyu, wato lokacin tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kano, Muhammadu Abubakar Rimi, Barau yake fitacce kuma wayayye kan harkar siyasar kasa ba ma ta jiha kawai ba. A lokacin fa wadanda a yanzu suke masa kallon shi sa’ansu ne, ko kusa da kafarsa ba su kai ba.

Saboda haka tun farkon farawa ma daga lokacin da mulkin dimukuradiyya ya dawo a shekarar 1999, bayan dadewa da a ka yi cikin mulkin soja, shi ba kifin rijiya ba ne.

A wancan lokacin na 1999 ya samu cin nasarar zama dan majalisar wakilai ta kasa, mai wakiltar karamar hukumar Tarauni, cikin birnin Kano.

Majalisar tarayya ta yanzu fa, bayan dawowar mulkin farar hula, ta samo tsayawa da kafar ta ne fa sakamakon yadda su Barau a wancan lokaci su ka tafiyar da harkar majalisar. Idan ka yi nazarin irin ayyukan jajircewa da ya yi a waccan majalisa, za ka san ashe dama can shi gwarzon dan siyasa ne.

A majalisar 1999 zuwa 2003, shine shugaban kwamitin rarraba dukiyar kasa, wato Appropriation Committee, lokacin marigayi Ghali Umar Na’Abba shine Kakakin majalisar wakilai din.

Tun fa da jimawa ma kafin dawowar mulkin farar hula a 1999, Barau wayayye ne, kwararre, dan siyasa mara tsoro, mai jajircewa kuma wanda yake da shaidar biyayya ga shugabanni da shugabanci.

Amman idan mutum ya na son sanin waye Barau a siyasar gidan tsohon gwamna Rimi ko ma a siyasar dake da alaka da marigayi Malam Aminu Kano, wato tun ma kafin 1999 kenan, to mutum ya tuntubi mutane irin su tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ko Hamza Darma ko Dauda Raula ko Aminu Nasidi ko Aminu Babba Dan Agundi, Sarkin Dawaki Babba a masarautar Kano da dai ire-irensu, jajirtattu ‘yan siyasar gaba-dai-gaba-dai.

Ai kuwa daga lokacin da ya zama Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa kuma, ya nuna kwarewa da jajircewa wajen tafiyar da ayyukan sa na majalisa. Dama ya shiga a matsayin wayayye, wanda kuma ya saba da siyasar kasa gaba daya. Shi fa gogewarsa da tasirinsa ba su tsaya kan mazabar sa kawai ba.

A na nan a na nan har ya zama an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa ta kasa. Su kan su abokan aikinsa sun lura da irin hobbasarsa wajen tafiyar da ayyukan majalisa da sanin yakamatan sa da kuma kishin kasar sa wajen ganin an samu daidaito da kuma hadin kan kasa.

Cikin Ikon Allah sau da yawa kuma ya na tsallake makirce-makirce da a ka kulla masa ba daya ba ba biyu ba ba uku ba. Amma cikin kiyayewar Allah, sai ya kasance kullum sai kara gaba yake cikin al’amuransa. Dama haka hanyar samun nasara take cike da samun cikas da hawa-da-sauka. Wasu lokuta na ba gaira-ba-dalili.

Kuma ya na kokarin gaske wajen ganin bai ba mazabarsa ta Kano ta Arewa da kuma jihar sa kunya ba, ta yadda yake gabatar da kudurori masu amfanin gaske ga majalisa. Wasu ma daga cikin kudurorin wadanda za su tallafawa ci gaban kasa ne kai tsaye. Baya ga na wadanda su ka shafi mazabarsa da jihar sa, da kuma nahiyarsa ta Arewa.

Wasu a tasu mahangar Sanata Barau fa ya samu wadannan damammaki ne saboda kujerar da yake kai ta mataimakin shugaban majalisar dattawa. Sau da yawa za a iya ce musu wannan gaskiya ne. Haka abin yake. Saboda ya kamata su ma su gane cewar a dalilin matsayin da yake kai din kuwa, to shi ba sa’ansu ba ne. Ba tsaransu ba ne. Saboda haka hada kai da shi da tunanin wai shi sa’an kowa ne, to tamkar karo ne da wani murgujejen dutse mai firgici. Kamar dai tarar aradu da ka.

Tun da babban burin wannan rubutun shine ya kawo yadda Sanata Barau ya yi shuhura kuma ya yi zarra a siyasar kasa gaba daya, ba wai iyakacin ta mazabar da yake wakilta ba, ko ta jihar Kano kawai, saboda haka ba zan tsomo batuttukan da su ka shafi abubuwan cigaba da more rayuwa da yake aiwatarwa a jihar Kano kawai ba.

Zan dan tsallaka na kawo kadan daga cikin kadan na ire-iren kudurorin da yake mikawa majalisa da su ka shafi cigaban wasu yankuna na kasar nan. Shi fa dan siyasa ne kuma abin alfahari ga kasa gaba daya, ba wai iyakacin dan tsukin da yake wakilta ba.

Kadan daga cikin ire-iren dokokin da majalisar dattawan ta yi sakamakon kudurorin da ya mika ga majalisar sune kamar haka, “Cyber Crimes (Prohibition, Prevention, etc) Bill (2023), Federal College of Education (Technical), Aghoro Bill (2019), in Bayelsa state, College of Mines and Geological Studies, Guyuk, Bill (2019), Federal University of Aquatic Studies, Ogharu, Bill (2019), in Anambra state and University of Maritime Studies, Oron, Bill (2017), Development Planning and Projects Continuity Bill (2023).”

Kuma fa a dalilin yadda ya zama ya shahara kan siyasar kasa gaba daya, tare da kasancewarsa shugaba nagari hakan ta sa a na gayyatarsa wasu al’amurran da su ka shafi wasu bangarorin kasar nan dan ya samu ya halarta kuma ya sa musu albarka.

Misali kwanan nan ya halarci bikin wani bikin shekara shekara da a ke yi na shekarar 2025 na Oronna Ilaro a jihar Ogun. Wanda ya je bikin ne tare da wasu manyan Sanatoci da su ka fito daga yankin. Wannan shi yake nuna maka yadda suke girmama shi a majalisar dattawa. Mutum ne mai salon shugabanci nagari.

Kuma a dalilin shi Sanata Barau din an samu wasu muhimman baki daga kasashen waje zuwa wajen bikin. An yi bikin ne a Asade Agunloye Pavilion Ground in Ilaro-Yewa, jihar Ogun. Shi Olu of Ilaro babban mai sarauta na Yewaland, His Royal Majesty, Oba (Dr) Kehinde Gbadewole Olugbenle, shine wanda ya shirya bikin.

Daga nan kuma ya karasa zuwa jihar Lagos dan taya tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Wannan fa duk a na nuni da cewar shi fa Sanata Barau mutum ne da ya yi fice a dukkan bangarorin kasar nan. Ba wai a waje daya kawai yake da kima da mutunci ba.

A dalilai irin wadannan ne ya sa har babbar jaridar nan ta kudancin Najeriya wato The Sun ta yi nazari ta gano ayyukan alheri da kuma tasiri da Sanata Barau yake da shi a siyasar Najeriya, har su ka zabe shi a matsayin wani babban mutum da za su karrama a karshen watan Janairu na shekara nai shigowa ta 2026. A can jihar Lagos.

An san hakan ne lokacin da Manajan Darakta na kamfanin jaridar Mr Onuoha Uke ya ja ragamar shugannin gidan jaridar kwanan nan zuwa ga ofishin Sanata Barau din har su ka shaida masa hakan. Sunan wannan girmamawa da za su yi masa ita ce, “The Sun Humanitarian Service Icon Award 2025.”

Saboda haka fa shi Sanata Barau ba sa’an wasu ba ne masu ganin ya tsone musu ido. Ba tsaran masu tasowa ba ne. Ko ma wadanda sun taso din amma ba su da kowane irin tasiri a tsarin siyasar jiha balle ma a ce ta kasa gaba daya. Shi din nan dai haka Allah Ya yi shi. Ba abinda ya rage ga abokan siyasa sai kallo. Yadda Ubangiji Ya tsara haka tsarin ke tafiya.

Anwar ya rubuta wannan daga Kano
Laraba, 29 ga Nuwamba, 2025

Share. Facebook Twitter LinkedIn Email Telegram WhatsApp

Related Posts

Defamation Against DSP Barau, Institutional: By Abba Anwar

From Enlightenment to Eclipse: Nigeria’s Democracy in an Age of Shadows: By Abbati Bako,psc,bsis,UK Alumnus

REBUILDING PUBLIC TRUST IN LEADERSHIP: THE NASIR IDRIS EXAMPLE IN KEBBI STATE: By Ibrahim A Jombali

Abdulaziz, the Arewa Media Summit, and Tinubu’s Renewed Hope Agenda – By Shehu Mustapha Chaji.

Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne: ‎ ‎Daga Abba Anwar ‎

Halacci Gadon Bacci: Daga Hajiya Fatima Abdullahi Dala, APC Women leader Kano.

Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Latest Posts

Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Umar Farouk Umar ya nada Sheikh Abdulkadir Jiyali a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa.

July 23, 2026

KEYAMO, MUSAWA CONFIRMED AS SPEAKERS AT 9TH NATIONAL TOURISM TRANSPORTATION SUMMIT & EXPO 2026: By Ado Salisu 

July 23, 2026

NSSF President Joseph elected ISF Africa continental president.

July 23, 2026
Advertisement
© 2026 ABKNEWS 24. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • Get In ToAhmad Musa ya yi ritaya daga Super Eagles bayan shekaru 15 yana buga kwallo.uch
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.