
MURTALA SULE GARO YA YI WA GWAMNA ABBA MARABA DA SHIGOWA APC
Tsohon dan takarar mataimakin gwamna a zaben shekarar 2023 a jam’iyyar APC, Alhaji Murtala Sule, ya yi wa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, maraba da shigowa jam’iyyar APC.
Alhaji Murtala Sule Garo ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Murtala Sule Garo ya bayyana cewar matakin da gwamnan ya dauka abin yabo ne, musamman domin samar da shugabancin hadaka da kuma tabbatar da dorewar kyakykyawan tsarin siyasa a jihar.
Garo ya kara da cewa dattaku da natsuwa da jajircewar da gwamnan ya nuna wajen inganta walwalar al’ummar jihar abubuwan da su ka cancanci yabo.
A cewarsa, fifita zaman lafiya da hadin kan al’umma akan banbance-banbacen jam’iyya da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, ya nuna kwarewarsa da zurfin tunaninsa.
Ya ce, “Shigowar mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC ta nuna hangen nesansa a siyasance da kuma zurfin tunaninsa akan irin kalubalan da ke tinkarar jihar da kasa baki daya.
“Ina da tabbacin shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin wannan jam’iyya tamu mai albarka zai kara karfafa jam’iyyar summanan akan kudirinta na inganta rayuwar al’umma tare da samar da hadin-gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Kano da gwamnatin tarayya domin amfanon al’ummar jihar.
“Yayin da nake yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf maraba da shigowa jam’iyyar APC, ina kuma jaddada goyon baya ga jam’iyyar tare da shirin yin aiki da mai girma gwamna da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar domin ci-gaba da samar da shugabanci na gari da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.”
Murtala Sule Garo

