
Murtala Sule Garo ya taya Musulmi murnar barka da sallah
Tsohon Dan Takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar APC a shekarar 2023, Murtala Sule Garo, ya taya al’ummar Musulmi barka da sallah.
Garo ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Yana mai kira ga al’umma da su sanya Najeriya cikin addu’o’insu.
A cewarsa, lokacin bubukuwan Sallah dama ce da kowa zai ya amfani da ita wajen kyautata mu’amularsa da Allah Madaukakin Sarki da Kuma tausaya marasa karfi.
Haka zalika ya zaburar da matasa da su dage wajen bada gudunmawa domin samawa Najeriya ci gaba mai dorewa.
Sanarwar ta ce, “Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
“Ina taya daukacin al’ummar Musulmin Najeriya murnar barka da sallah. Wannan wani lokaci ne mai matukar muhimanci a tarihin addinin Musulinci. Ya na nusar da mu tsananin biyayyar Annabi Ibrahim (amincin Allah ya tabbata a gareshi) ga Allah subhanahu wa ta’allah. Manyan darusan da za mu koya daga gareshi sun hada da kan’kan da kai da hakuri da kuma biyayya ga Allah.
“A yayinda muke gudanar da bukukuwan sallah, ina karfafawa ‘yan Najeriya gwiwa da mu dage da kaunar juna da tausayawa na kasa da mu da mara karfi da wanzar da zaman lafiya.
“Za mu iya kawo Najeriya ci gaba ne kawaii dan mu ka dunkule wuri guda da tabbatar da adalci a tsakaninmu.
“Ina kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan dama wajen yiwa shugabanni da jami’an tsaro addu’a, musamman wadan da su ke aiki ba dare ba rana wajen wanzar da zaman lafiya
“Ina kira da matasanmu da kada su yanke kauna da kuma su tabbatar da sun ci gaba da bada gudunmawarsu wajen gina wannan kasa. Wannan kasar na bukatarsu fiye da ko wane lokaci.
“Haka zalika kada mu manta da marasa karfin cikinmu da ‘yan gudun hijira da wadan da su ke cikin halin kaka-nikayi
“Ina rokon Allah da ya kawo mana zaman lafiya da yalwar arziki da hadin kai da kaunar juna. Allah ya karbi ibadinmu. Amin.”
Eid-el-Fitr: Murtala Sule Garo felicitates with Muslims
Former APC’s 2023 deputy governorship candidate, Murtala Sule Garo felicitated with Muslims on the occasion of Eid-el-Fitr celebrations.
In a statement on Friday, Garo urged Muslim faithful to use the opportunity for pray for Nigeria, particularly its leadership and security personal who sacrifice their lives to protect the citizens.
He, however, called on youth to he steadfast in their pursue of definitive future.
The statement reads, “In the name of Allah, the Most Beneficent, the Most Merciful.
“I extend my warmest greetings and heartfelt felicitations to Muslim faithful across Nigeria and beyond as we celebrate this joyous and sacred occasion of Eid-el-Fitr.
“Sallah is a profound reminder of faith, sacrifice, obedience and unwavering trust in Allah. It commemorates the noble example of Prophet Ibrahim (AS), whose devotion teaches us the virtues of submission, patience and selflessness.
“As we mark this blessed season, I urge all Nigerians to reflect on the deeper lessons of Eid-el-Fitr, compassion for one another, generosity toward the less privileged and commitment to peace and unity.
“True progress can only be achieved when we work together across religious, ethnic and political lines to build a nation anchored on justice, equity and opportunity for all.
“Let us use this moment to pray for our leaders, our security agencies and those working tirelessly for the stability and advancement of our country.
“To our youths, I encourage you to remain hopeful and committed to positive engagements. Your energy, creativity and patriotism are essential to shaping a brighter future.
“As families gather to celebrate, let us remember those who are less privileged, the displaced and those facing hardship. May our acts of kindness and charity reflect the true spirit of Eid-el-Fitr.
“I pray this Sallah brings renewed hope and peace in our hearts, prosperity in our homes and lasting unity to our beloved nation. May Allah accept our prayers, our sacrifices and our good deeds.
“Eid-el-Fitr Mubarak to you all

