
Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da jiha da Kana Nan Hukumomi da su mayar da hankali domin kare rayuka, Lafiya da Dukiyoyin Al’uma – Sarki Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da Jawabinsa na Barka da Sallah Jim kadan da idar da sallah Idi Karama a fadarsa dake Gidan Sarki na Nassarawa a birnin Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya Zama wajibi shugabanni suyi la’akari da yanayin rayuwa da Al’uma suke ciki akan abubuwan da sukafi bukata.
Sarkin ya bukaci su kasance masu yiwa Shugabanni addu’a da Kuma kyautata musu zato akan dukkanin al’amuran shugabancinsu.
Yayi addu’ar Allah ya cigaba da Tabbatar da alheri tareda bawa shugabannin ikon aiwatar da abubawan da sukafi damun Al’uma Musamman harkar tsaro da saukin abinci da kayan masarufi.
Ya godewa Gwamnatin Tarayya da ‘Yan Majalisar Dattawa da na tarayya sa ‘yan Majalisun jiha bisa irin Taimakon da suka yiwa Jama’a a lokacin watan azumin Ramadan, inda yayi fatan zasu cigaba davirin wannan taimako.
Sarkin Kano ya godewa Malamai da Limamai bisa fadakarwa tareda kira Nan gaskiya da sukayi a lokacin azumi akan tafarki na gaskiya.
Kazalika Sarkin ya yabawa ‘yan kasuwa da attajirai bisa gudumawa da suka bayar inda yayi fatan zasu cigaba da ganin kayan abinci dana masarufi sun cigaba dayin saukin ta yadda Al’uma zasu amfana.
Alhaji Aminu Ado Bayero daga nan ya taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Jami’an Gwamnati da sauran Al’uma Muranar Barka da Sallah.
Sa hannu.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada Labàrai na Sarkin Kano
Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL.
20/03/2026
1 Shawwal, 1447 AH.

