Muna da kwarin gwaiwar doke Enyimba a wasanmu na farko a NPFL-Ladan Boss
Babban mai horar da Ƙungiyar Kwallon Ƙafa ta Barau FC, Isah Ladan Bosso, ya bayyana kwarin gwiwar sa na cewa zasu samu sakamako mai kyau a wasansu na farko da kungiyar kwallon kafa ta Enyimba, a sabuwar kakar 2025-2025 ta gasar firimiya ta Najeriya mai daraja ta farko (NPFL).
Yayin wata hira da Ahmad Hamisu Gwale, Daraktan Yaɗa Labarai na Barau FC, Bosso ya bayyana farin cikinsa da gamsuwa da shirin da suka yi gabanin wannan babban wasa da masoya kwallon kafa a fadin kasar nan suke son gani.
Sabon zangon gasar NPFL na shekarar 2025/26 ya fara ne a ranar Juma’a, inda Barau FC za ta karɓi bakuncin Enyimba FC a gobe Lahadi, 24 ga watan Agusta, 2025, a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
Ƙungiyar wacce ake mata lakabi da Maliya Boys, ta dai samu damar zuwa gasar NPFL a wannan kakar, na fatan farawa da kyau tun a farko.
“Ina farin ciki da kasancewa ta nan jihar kano tare da kasancewa da Barau FC. Mun zo nan ne domin kawo sauyi, kuma za mu tabbatar mun ci gaba da samun nasarorin da aka riga aka samu tare da Barau FC,” in ji Bosso.
“Na yarda mun shirya. Ƴan wasan suna cikin koshin lafiya kuma suna da ƙwazo. A gare ni, fafatawa da Enyimba ba sabo ba ne, amma ina tabbatar wa da magoya bayanmu cewa a ƙarshen wasan zamu sami nasara.”


