
Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar ayyuka ta kasa NPC Hon. Dr. Baffa Babba Danagundi yayin da yake jawabi a wajen taron Samar da jari da kayan Sana’a ga Al’ummar Nijeriya a gaban Ministan Kwadago da Nagartar Ayyuka na kasa.
Taron Wanda ya gudana a Babban Birnin Tarayya Abuja, kuma an shirya shine domin kaddamar da Samar da jari da kayan koyon Sana’a ga al’ummar Kasa musamman masu kanan jari.
A nasa jawabin Babban Mininstan Kwadago da Nagartar Ayyukan ya yabawa Babban Daraktan na NPC Dr. Baffa Babba Dan’agundi bisa yadda yake kokari a harkokin siyasa da wajen tallafawa da koyar da sana’oi ga Al’ummar Kasa musamman a yankin arewa maso yamma da tarayyar ƙasa baki ɗaya,
Ministan kuma ja hankalin mahalarta taron da suyi koyi da shi wajen hidima ga masoya shugaban kasa.
Taron dai ya samu halattar manyan bakin da suka hadar da Mininstan Ma’aikatar Kwadago Muhammadu Maigari Dingyadi da Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, da Kuma Shugaban Kwamitin Kwadago na majalisar Dattijai Senator Sulaiman Nazif, da takwaransa na majalisar wakilai Hon. Adegboyega Adefarati.
Sauran sun hadar da Shugaban hukumar Samar da ayyukanyi ta kasa His Excellency Salis Agara da Babban Sakataren Ma’aikatar Kwadago ta kasa
Dr. Salihu A. Usman.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

