
Majalisar Dokokin Kano Ta Sanya Ranar Tantance Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Gwamna
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sanya ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026 domin tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano.
Kakakin Majalisar, Hon. Jibrin Ismaila Falgore ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na wannan rana ta laraba.
Kakakin majalisar ya karanta wasikar da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya turawa majalisar ta bukatar tantancewa tare da amince masa ya nada Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakinsa.
Da dumi-dumi: Gwamna Abba ya miƙa sunan Murtala Garo ga Majalisa domin naɗa shi mataimakin gwamna
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mika sunan Murtala Sule Garo domin zama mataimakin gwamna, bayan murabus din Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a watan da ya gabata.

