
Majalisar Dokokin Kano Ta Musanta Yunƙurin Tsige Mataimakin Gwamna
Majalisar Dokokin Kano ta musanta rahotannin da ke iƙirarin cewa ana shirin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, tana mai bayyana hakan a matsayin zargin da ba shi da tushe balle makama.
Mai magana da yawun Kakakin Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, inda yace babu wata tattaunawa, ƙuduri ko yunƙuri a cikin Majalisar da ke nufin tsige Mataimakin Gwamnan.
Zuwa yanzu dai babu wani martani da Mataimakin Gwamnan ya mayar dangane da wannan zargin ba, Sai dai majiyoyi sun tabbatar da cewa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum a hukumance.

