
Kotun koli ta sanya ranar cigaba da sauraron karar dambarwar masarautar Kano
Kotun Kolin Kasarnan da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta sanya ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 2027 domin ci gaba da sauraren karar da Alhaji Aminu Babba Dan agundi ya shigar inda ya ke kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara.
A zaman kotun na yau Litinin, lauyan mai kara, ya gabatar da rokon su kuma dukkanin lauyoyin da ke kare wadanda ake kara ba su yi suka ba amma shi lauyan majalisar dokokin Kano Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci, ya bukaci suka amma suka ce damar su ce.
Yayin da daga karshe kotun ta daga zaman zuwa shekara guda domin ci gaba da shari’ar.
Kamar yadda Alhaji Aminu Babba Dan agundi yake yiwa manema labarai Karin haske
Tun da farko dai Alhaji Aminu Babba Dan agundi ne ya shigar da kara inda ya ke kalubalantar matakim da majalisar dokokin Kano ta yi na cire Sarkin Kano Aminu Ado bayaro, inda hakan ta sa ya garzaya kotun tarayya da ke Kano domin nuna damuwarsa a matsayinsa na daya daga cikin masu nada Sarki, kotun ta kuma tabbata da cewa ya na da hurumi.
Su kuma wadanda ya kai kara suka garzaya kotun daukaka kara ita kuma kotun ta ce bas hi da hurumin yin hakan, saboda haka ya garzaya kotun Koli domin ta tabbatar da hukuncin

