
Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Mataimakin Gwamnan Kano Kan Tsige Shi
Babbar Kotun tarayya ta yi watsi da bukatar da mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, ya gabatar na neman dakatar da majalisar dokokin jihar Kano daga yunkurin tsige shi.
Mai shari’a S. M. Shaibu ne ya yanke wannan hukunci, inda kotun ta ce mai karar bai cika ka’idoji da sharudan da doka ta tanada ba domin samun umarnin wucin gadi.
Haka kuma, kotun ta umarci mataimakin gwamnan da ya mika takardun karar ga wadanda ake kara, domin su samu damar kare kansu a gaban kotu.
A wani bangaren kuma, rahotanni sun bayyana cewa tun a ranar 11 ga watan Maris 2026, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta samu wani umarni daga kotu da ke hana Mataimakin Gwamnan daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga ayyukan majalisar kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

