
Kasashe na iya kin amincewa da sabbin jakadun Tinubu saboda karancin wa’adin aiki
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin sabbin jakadun da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daya nada na iya fuskantar matsalar kin amincewa daga kasashen da aka tura su, sakamakon karancin lokacin wa’adin aikinsu.
Manyan jami’ai a Fadar Shugaban Kasa da kuma ma’aikatar harkokin diflomasiyya sun bayyana cewa Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar nan na fuskantar kalubale wajen samun amincewar hukuma daga kasashen da za su karbi jakadun ga wasu daga cikin wadanda aka zaba.
A cewarsu, wasu kasashe na bukatar jakada ya samu akalla wa’adin aiki na shekara daya ko biyu, wanda yawanci ake daura shi da tsawon wa’adin gwamnatin kasar da ta aike shi.
Wani babban jami’in diflomasiyya da ya nemi a sakaya sunansa saboda muhimmancin batun ya ce:
Babbar matsalar da muke fuskanta yanzu ita ce kasashe da dama, misali Indiya, na iya cewa idan wa’adin jakada bai kai shekara daya ko biyu ba, za su samu matsala wajen karbarsa. A yawancin lokuta, ana kallon wa’adin aiki har zuwa karshen gwamnatin da ke kan mulki.
Tun da zaben shugaban kasa na gaba zai gudana a watan Fabrairun 2027, kuma wa’adin farko na Shugaba Tinubu zai kare a watan Mayun shekarar, jami’an sun bayyana damuwa cewa wasu kasashe ba za su so karbar jakadun da wa’adinsu ya yi kankanta ba a wannan lokaci.

