
“Ya ku Al’umar Najeriya !!!
Kamar yadda kuka sani, na dage halartar taron G20 a Afrika ta Kudu domin in tabbatar da cewa ana samun cikakkiyar kulawa da adalci kan al’amuran tsaro a Najeriya.
Na yi matuƙar farin cikin sanar da cewa, sakamakon ƙoƙari da jajircewar hukumomin tsaro, dukkan mutane 38 da aka yi garkuwa da su a Cocin Christ Apostolic da ke Eruku, Jihar Kwara, sun samu ‘yanci cikin koshin lafiya.
Haka kuma, an ceto dalibai 51 daga cikin waɗanda suka bace a harin da aka kai Makarantar Catholic da ke Jihar Neja.
Ina ci gaba da sa ido kan dukkan matakan tsaro a faɗin ƙasar nan tare da karɓar rahotanni kai tsaye daga jami’an tsaro da ke bakin aiki.
Ina tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba. Tsaro haƙƙin kowane ɗan Najeriya ne , kuma a ƙarƙashin wannan gwamnati, za mu ci gaba da kare rayukan jama’a da tabbatar da zaman lafiya.”

