
“Ya ku Al’umar Najeriya !!!
Kamar yadda kuka sani, na dage halartar taron G20 a Afrika ta Kudu domin in tabbatar da cewa ana samun cikakkiyar kulawa da adalci kan alâamuran tsaro a Najeriya.
Na yi matuĆar farin cikin sanar da cewa, sakamakon ĆoĆari da jajircewar hukumomin tsaro, dukkan mutane 38 da aka yi garkuwa da su a Cocin Christ Apostolic da ke Eruku, Jihar Kwara, sun samu âyanci cikin koshin lafiya.
Haka kuma, an ceto dalibai 51 daga cikin waÉanda suka bace a harin da aka kai Makarantar Catholic da ke Jihar Neja.
Ina ci gaba da sa ido kan dukkan matakan tsaro a faÉin Ćasar nan tare da karÉar rahotanni kai tsaye daga jamiâan tsaro da ke bakin aiki.
Ina tabbatar wa âyan Ćasa cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba. Tsaro haĆĆin kowane Éan Najeriya ne , kuma a ĆarĆashin wannan gwamnati, za mu ci gaba da kare rayukan jamaâa da tabbatar da zaman lafiya.”

