
Jam’iyyar mu ba wata ƙungiya ce ta mutum daya ba – NDC
Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa ba wata ƙungiya ce ta mutum ɗaya ko kuma wata kafa ta wucin-gadi da za a yi amfani da ita a watsar ba, tana mai jaddada cewa jam’iyya ce mai cikakken tsari da za ta dore kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Osa Director, ya fitar, ya ce Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) ya sake tabbatar da cewa jam’iyya ita ce ke da iko mafi girma, kuma duk shirye-shirye, manufofi da naɗe-naɗen gwamnatocin da aka zaɓa a ƙarƙashinta dole ne su kasance tare da tuntubar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa duk ƙungiyoyi da ƙungiyoyin sa-kai masu alaƙa da ita za su kasance ƙarƙashin kulawa da jagorancin jam’iyyar, ba tare da gudanar da ayyuka daban da tsarin jam’iyyar ba.
NDC ta sanar da kafa kwamitin sulhu domin sasanta membobin da ke da ƙorafe-ƙorafe, bayan wasu ‘yan takara sun zargi jam’iyyar da kakaba musu ‘yan takara a zaɓukan fidda gwani.
Haka kuma, jam’iyyar ta ce za ta kafa ƙa’idoji ga jami’anta da ‘yan takara, tare da ƙarfafa bin doka da gaskiya wajen tafiyar da harkokin kuɗi.
NDC ta kuma jaddada cewa duk gudummawar kuɗaɗen kamfen da sauran tallafi dole ne su rika shiga ta asusun jam’iyyar da aka tanada, yayin da ake sa ran ‘yan takara su bayyana dukkan kuɗaɗen da suka tara da yadda aka kashe su domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

