
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kano Ta Fara Bincike Kan Tsohon Shugaban Ma’aikata
Hukumar ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jama’a (PCACC) ta fara bincike kan zarge-zargen da ake yi wa tsohon Shugaban Ma’aikata na Jihar Kano, Abdullahi Musa, kan zargin cire kuɗi daga albashin ma’aikata ba tare da amincewarsu ba.
Rahotannin sun nuna cewa jami’an hukumar sun kuma rubuta sanarwa da fenti ja a ƙofar gidansa da ke cikin rukunin gidaje na Almukab City da ke ƙaramar hukumar Kumbotso.
Gwamna Yusuf Ya Umarci A Binciki Abdullahi Musa Kan Zargin Rage Albashi na ₦1.5bn
An ruwaito cewa rubutun ya ce: “A ƙarƙashin Bincike, PCACC Kano 18/05/2026.”
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike don gano gaskiyar da ke tattare da zarge-zargen da kuma tantance matakan da suka dace idan an tabbatar da zarge-zargen.

