Daga Murtala Baba:

Hukumar Da’ar Ma’aikata Ta Kasa Shiyyar Kano ( Code Of Conduct Bereau ) Ta Fitar Da Sanarwar Gargadi na Karshe ga Masu Rike Da Mukaman Gwamnatin Jihar Kano.
Shugabar Hukumar Dake Kula Da Kano Hajiya Hadiza Larai Ibrahim Ce Ta Sanar Da Hakan a Wata Sanarwa Da Ta Fitar.
Tace Yanzu Haka Hukumar Ta Tattara Sunayen Mutane Sama Da 70 Da Zata Dauki Mataki Akansu Kamar Yadda Doka Ta Tanada
Wadanda Suke Cikin Sunayen da Hukumar Zata Dauki Mataki akwai Kwamishinoni, Da Mnaging Directors, Da Director Generals, Da Masu Baiwa Gwamna Shawara da Wasu Kansiloli
Acewar Hajiya Hadiza Larai Ibrahim, Rashin Zuwa Hukumar Domin Cike Form Din ( CCB ) Wanda Dokar Ƙasa Tace Wajibi Duk Wani Mai Rike Da Mukami Sai Ya Bayyana Kaddarorin sa a Lokacin da aka Naɗa Shi Da Kuma Bayan Ya Sauka.
Kin Yin Hakan zai Kai Ga Gurfanar da Mutum Gaban Kotu, Tare Da Haramta Masa Rike Duk Wani Mukamai Ko Shiga Harkar Siyasa Na Sama Da Shekaru 10.
Haka Kuma Duk Wanda aka Sauyawa Wajen aiki Daga Wata Hukuma Zuwa Wata Ko a Sauya Masa Matsayi Wajibi Yaje Hukumar Dake Sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Kan Titin Katsina Road.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

