
Hukumar Hizba ta hana Tashe da kidan Gwuro a Fadin jihar Kano Sheikh Dr mujahid Amenudeen.
Babban Kwamandan hizba ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne yake wannan jawabi ta bakin mukadashin babban Kwamandan hizba ta jihar Kano Sheikh Dr mujahid Amenudeen .
Kazalika Dr mujahid yace wannan matakin nazuwa ne bayan zaman da sauran masu ruwa da tsaki na jihar Kano don inganta tsaro da matunci jama’ar Kano .
Kuma akwai hukunci Mai tsauri ga Wanda yayi kunnan kashi ga wannan matakin da hukumar ta dauka.

