
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ita ce ta sanar da wannan mataki, inda ta ce ba za ta bari direbobin Keke Napep ɗin na ɗaukar mata a gaban Keken ba saboda ya saɓa wa shari’ar musulunci
Ta kara da cewa muddin al’umma na buƙatar samun rayuwa mai yalwa, to tilas ne sai sun ƙaurace wa saɓon Allah wanda kuma cakuɗuwa maza da mata haramtacciyar lamari ne a addinin musulunci, don haka ne ta ce ta ɓullo da wannna tsari don bin umarnin Allah
Hukumar ta ce ba ita kaɗai za ta yi wannan aiki ba, za ta haɗa hannu da sauran hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa a Jihar don tabbatar da ganin cewa dokar ta yi aiki
Daga nan sai ta gargadi direbobin keke Napep ɗin da su bi wannan umarnin na hukumar sau da ƙafa don gudun faɗawa fushinta.

