
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sha alwashin kubutar da daliban makarantar sakandaren ‘yammata da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
Ministan yada labarai Muhammad Idris shi ne ya sanar da hakan a wata wasika da ya aike wa manema labarai. Ya ce gwamnati na tattaunawa da dakarun wanzar da zaman lafiya na ECOWAS da AU domin tunkarar matsalar tsaro a Najeriya.

