
Gwamnatin Tarayya ta amince da gina Titin Jirgin Kasa na kwaryar Birni (Metropolitan Rail Service) kan kudi naira tiriliyan ɗaya a Jihar Kano, wani babban aiki da ake sa ran zai sauya harkar sufuri a birnin tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar.
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa amincewar da Gwamnatin Tarayya ta bayar na gina titin jirgin kasan na da nufin rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta harkar sufuri a cikin birnin Kano.
A wata sanarwa da kakakin Gwamnan Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga tawagar Jihar Kano da ta halarci Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa ta shekarar 2025 da aka gudanar a Jihar Borno.
A cewar Gwamnan, aikin jirgin kasan zai samar da ingantaccen tsarin sufuri na zamani kuma mai araha wanda zai haɗa manyan yankuna a cikin birnin, tare da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da bunƙasa kasuwanci da zuba jari.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na sake daidaita alaƙa da Gwamnatin Tarayya ya samo asali ne domin jawo muhimman ayyukan raya ƙasa da za su inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.
Ya bayyana aikin hanyar jirgin kasan a matsayin wani muhimmin gagarumin aiki da zai mayar da Kano cibiyar sufuri a Arewacin Najeriya tare da inganta rayuwar al’umma.
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin Tarayya domin tabbatar da aiwatar da aikin cikin sauƙi da gaskiya, tare da nuna godiyarsa ga Gwamnatin Tarayya bisa wannan shiri.

