
Yanzu Dai Duk Wanda Yake San Zuwa aikin aikin hajjin bana daga arewa Maso Yamma zai biya naira Miliyan 7.6
Sai kuma waɗanda Zasu je daga Jihohin Adamawa da Borno za su biya Naira miliyan 7.5
Sabon Farashin Wanda Shugaban hukumar NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ke Jagoranta ne ya shaida wa Manema Labarai
Pakistan Ya ce an Samu Ragin ne Sakamakon Umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu na Rage Kuɗin aikin Hajjin
A Wannan Sabon Farashin jihohin da ke shiyyar Borno da Adamawa za su biya Naira 7,579,0202 sabanin naira 8,327,125 da hukumar ta sanar a baya.
Sai Jihohin Arewa kuma sabon farashinsu shi ne naira 7,669,769 sabanin naira 8,457,685 da aka sanar a watannin baya.
Jihohin kudancin Nijeriya kuwa za su biya naira 7,991,141 sabanin naira 8,784,085.
Haka Kuma Hukumar Ta Sanar da 5 ga watan Disamba ta zama ranar karshe da duk mai sha‘awar zuwa hajji daga Nijeriya zai biya kudinsa.

