
Gwamna Yusuf Ya Kaddamar da Rijistar APC ta Intanet a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da aikin rijistar jam’iyyar APC ta hanyar intanet (e-registration) a jihar, inda ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin yunkuri na karfafa dimokuradiyyar cikin gida da kuma kara yawan mambobin jam’iyyar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya kaddamar da aikin ne a ranar Litinin a Dakin Coronation da ke Gidan Gwamnatin Kano, jim kadan bayan komawarsa jam’iyyar APC.
A wajen taron, gwamnan ya samu rakiyar ‘yan Majalisar Wakilai takwas, ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano 21, da mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar.
Gwamna Yusuf ya ce rijistar ta intanet tsari ne mai gaskiya, mai bai wa kowa dama, kuma na zamani, wanda aka kirkira domin inganta tafiyar da harkokin jam’iyyar da kuma tabbatar da sahihin bayanan mambobinta.
Ya bayyana cewa tsarin zai taimaka wajen kawar da maimaita rijista, da kara inganci, tare da samar da cikakken kundin bayanai da zai nuna karfin jam’iyyar APC a matakin mazabu, kananan hukumomi da daukacin jihar baki daya.
Gwamnan ya bukaci mambobin jam’iyyar, magoya baya da masu sha’awar shiga APC da su fito su yi rijista domin tabbatar da nasarar shirin.
Haka kuma, ya yaba wa shugabannin jam’iyyar APC a matakin kasa, jiha da kananan hukumomi bisa rungumar fasahar zamani wajen inganta tafiyar da harkokin jam’iyyar, yana mai jaddada bukatar bin ka’idoji domin aikin ya gudana cikin sauki da sahihanci.
Sanarwar ta kara da cewa za a gudanar da aikin rijistar ta intanet a dukkan mazabu na Jihar Kano, inda mambobi za su samu damar yin rijista, sabunta bayanansu, da kuma sake tabbatar da kasancewarsu ‘yan jam’iyyar APC.

