
Amincewar ta biyo bayan ganawar da tawagar gwamnatin jihar ta yi da Oba Ladoja a ranar Laraba, da kuma mambobin majalisar ba da shawara ta Olubadan din.
Da yake tabbatar da amincewar, mai taimakawa Oba Ladoja kan harkokin yada labarai, Cif Adeola Oloko, ya ce an tsayar da nadin sarautar ne a ranar 26 ga watan Satumba, a dakin taro na Mapo Hall, Oja-oba, dake birnin Ibadan.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Ladoja, tsohon gwamnan jihar Oyo, ya koma Ibadan ne a ranar Litinin bayan ya kwashe makonni yana gida.
Majalisar ba da shawara ta Olubadan ta nada shi a ranar 4 ga watan Agusta biyo bayan rasuwar marigayi Oba Owolabi Olakulehin a ranar 7 ga watan Yuli.
𝙳𝙾𝙼𝙸𝙽 𝙽𝙴𝙼𝙰𝙽 𝙺𝙰𝚁𝙸𝙽 𝙱𝙰𝚈𝙰𝙽𝙸 𝙺𝙾 𝙱𝙰𝚈𝙰𝚁 𝙳𝙰 𝚃𝙰𝙻𝙻𝙰 𝙺𝙾 𝚂𝙷𝙰𝚆𝙰𝚁𝙰 𝚂𝙰𝙸 𝙰 𝚃𝚄𝙽𝚃𝚄𝙱𝙴𝙼𝚄 𝚃𝙰 𝙷𝙰𝙽𝚈𝙰𝚁 𝚃𝚄𝚁𝙰 𝚂𝙰𝙺𝙾𝙽 𝚆𝙷𝙰𝚃𝚂𝙰𝙿𝙿 𝙰 𝚆𝙰𝙽𝙽𝙰𝙽 𝙻𝙰𝙼𝙱𝙰𝚁 𝟶𝟿𝟶𝟿𝟿𝟸𝟸𝟸𝟸𝟷𝟷
𝚊𝚋𝚔𝚗𝚊𝚒𝚜𝚊𝟷𝟶𝟶@𝚢𝚊𝚑𝚘𝚘.𝚌𝚘𝚖

