
Ganduje ya ziyarci Kano dan duba aikin masallatai da makarantu na Islamiyya da Gidauniyarsa ta Gina
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, CON, ya duba ayyukan gina masallatai da makarantu na Islamiyya da Gidauniyar Ganduje ta gina a sassa daban-daban na Jihar Kano.
Daga cikin ayyukan da tsohon gwamnan ya duba sun haɗa da:
1. Masallacin Juma’a da makarantar Islamiyya a Bachirawa, Karamar Hukumar Ungogo. Bayan kammala aikin, Sheikh Lawal Triumph zai rike masallacin.
2. Masallacin sallar kullum guda biyar da makarantar Islamiyya a Bachirawa, Karamar Hukumar Ungogo.
3. Masallacin Juma’a da makarantar Islamiyya tare da ɓangaren mata a Lodge Road, Karamar Hukumar Nassarawa.
Yayin duba ayyukan, Dakta Ganduje ya nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa damar da ya ba shi da kuma Gidauniyarsa wajen gudanar da waɗannan ayyuka.
Gidauniyar Ganduje ƙungiya ce mai zaman kanta (NGO) wacce ta ke mai da hankali wajen bunƙasa addinin Musulunci da kuma tallafa wa marasa galihu da al’umma masu rauni a Najeriya. Ta gina daruruwan masallatai da makarantu na Islamiyya a sassa daban-daban na ƙasar.
A yayin wannan ziyarar duba ayyuka, Ganduje ya samu rakiyar ɗan takarar gwamna na APC a 2023 kuma Shugaban Hukumar Kula da Lamunin Gida na Ƙasa (Federal Mortgage Bank), Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, tsohon shugaban ma’aikatansa, Kwamared Muhammad Garba, Ministar FCT mai taimako (State), Hajiya Mariya Mahmud, Manajan Darakta na Hadejia Jama’are, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi, Rt. Hon. Farouk Lawan, Sheikh Lawal Triumph, Barista Ishaq Adam, da sauran fitattun mutane.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 09099222211 ko abknaisa100@yahoo.com


