
Ganduje da APC sun yiwa Gwamnan Kano Yusuf Maraba cikin APC, sun shirya karbarsa hannu Biyu – Abdullahi Abbas
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta bayyana shirinta na tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf idan ya yanke shawarar barin NNPP ya koma APC, abin da ke tayar da cece-kuce a siyasar jihar.
Rahotanni na cewa gwamnan na shirin canza sheƙa zuwa APC nan da farkon watan Janairu 2026, musamman domin shirye-shiryen babban zabe na 2027.
Abknews24 ta rawaito cewa wannan batu ya jawo muhawara tsakanin shugabannin siyasa da magoya baya a jihar.
A cikin wata sanarwa da shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya fitar yace Shugabannin APC a Kano sun bayyana cewa shigar gwamnan jam’iyyar zai ƙara ƙarfin APC a jihar, musamman wajen samun rinjaye a zaben 2027, inda suke ganin wannan mataki zai bai wa jam’iyyar fa’ida sosai.
Sai dai jam’iyyar NNPP a jihar ta bayyana cewa ba za ta amince da wannan shiri ba. NNPP ta yi kira ga gwamnan da ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar, tana mai cewa barin jam’iyyar zai zama cin amanar ƙuri’un masu zabe.
Masana siyasa na cewa wannan motsi na iya sauya taswirar siyasa a Kano, inda APC ke shirin amfani da damar wajen ƙara tasiri a tsakanin al’umma kafin babban zabe na shekara mai zuwa

