
El-Rufa’i Ya Kafa Tubalin Tsaro da Ilimi a Kaduna – Jafaru Sani
Daga SHEHU YAHAYA
Tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kaduna, Malam Jafaru Ibrahim Sani, ya bayyana cewa babu shakka tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i, ya kafa tarihi wajen samar da tsaro da kuma bunkasa harkokin ilimi a lokacin da yake jagorantar al’amuran jihar.
Malam Jafaru Ibrahim Sani ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai . a cewarsa, gwamnatin El-Rufa’i ta taka muhimmiyar rawa wajen rage ayyukan ta’addanci, fashi da makami da kwacen waya da suka addabi al’ummar jihar a baya.
A cewarsa, a lokacin mulkin El-Rufa’i, an samu gagarumin sauki a hare-haren ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a sassa daban-daban na jihar, lamarin da ya bai wa gwamnati damar aiwatar da manyan ayyukan raya qasa ba tare da tangarda ba. Ya ce wannan sauqin tsaro ne ya taimaka wajen bunqasa ayyukan ci gaba a fannoni daban-daban da suka haxa da ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da harkokin qananan hukumomi.
Tsohon kwamishinan ya kara da cewa bangaren ilimi ya amfana matuqa a lokacin gwamnatin El-Rufa’i, inda aka gina makarantu, aka inganta tsarin koyarwa, tare da xaukar malamai masu kwarewa domin ceto harkar ilimi daga halin da take ciki. A cewarsa, waxannan matakai sun taimaka wajen farfado da darajar ilimi a Jihar Kaduna tare da samar da kyakkyawan tushe ga ci gaban matasa.
Malam Jafaru Ibrahim Sani, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC, ya nuna takaicinsa matuqa kan yadda gwamnatin Jihar Kaduna ta yanzu ke tafiyar da harkokin tsaro. Ya zargi gwamnatin da yin sakaci da rikon sakainar kashi, wanda a cewarsa hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da rashin tabbas, musamman a yankunan karkara.
Ya ce yadda hare-haren ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka ke kara yawaita a wasu sassan jihar ya nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a yana mai cewa wannan yanayi ya hana aiwatar da ayyukan ci gaba yadda ya kamata tare da jefa jama’a cikin mawuyacin hali na tattalin arziki da zamantakewa.
Akan hakan Malam Jafaru Ibrahim Sani ya bayar da tabbacin cewa al’ummar Jihar Kaduna za su yi watsi da jam’iyyar APC a zaven shekarar 2027, su rungumi jam’iyyar ADC domin ceto jihar daga halin da take ciki. Ya ce ADC ta zo da sabbin tsare-tsare da manufofi da za su dawo da tsaro, ci gaba da walwala ga al’umma.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su hada kai, su guji rarrabuwar kawuna, tare da amfani da damarsu ta dimokuradiyya wajen zavar shugabannin da za su fifita muradun jama’a a kan na kansu.
A karshe, Malam Jafaru Ibrahim Sani ya jaddada cewa Jihar Kaduna na bukatar shugabanci nagari, tsari mai kyau da jajircewa domin dawo da zaman lafiya da ci gaban da al’umma ke fata, yana mai bayyana cewa hakan ne kazai zai tabbatar da makoma mai kyau ga jihar da ‘ya’yanta.
Jafaru Sani Wanda kuma shine shugaban jamiyyar hadaka ta ADC na shiyyar Arewa maso yamma ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin dawo da ci gaba da tsare-tsaren da tsohuwar gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa’i ta assasa, musamman a vangarorin tsaro, ilimi da raya kasa, idan har jam’iyyar ta karvi ragamar mulkin Jihar Kaduna a shekarar 2027 mai zuwa.
A cewarsa, ADC ta kammala shirye-shirye na samar da tsayayyen tsarin tsaro, wanda zai hada da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da al’umma, tare da amfani da sabbin dabaru domin dakile ta’addanci, fashi da makami da sauran laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar jihar. Ya ce jam’iyyar ta quduri aniyar tabbatar da cewa rayuka da dukiyoyin jama’a sun samu cikakken kariya, domin ba tare da tsaro ba, babu ci gaba mai ɗorewa.

