
ECOWAS na shirin samar da jami’an tsaro na sa-kai dubu 260 don yakar ta’addanci a Afirka
Kungiyar Cigaban Tattalin Arziki ra Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta baiyana shirin ta na samar da jami’an tsaro na sa-kai dubu 260 don yakar ta’addanci a nahiyar Afirka.
Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya baiyana hakan a taron hafsoshin tsaro na 2025 a Abuja.
Touray, wanda ya samu wakilcin Abdel-Fatau Musah, Kwamishinan harkokin siyasa na ECOWAS, ya ce wannan wani mataki ne na rage harkokin ta’addanci a Afirka.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 09099222211 ko abknaisa100@yahoo.com

