
Mai girma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa na bankin bada lamunin gina gidaje na tarayyar Najeriya, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya halarci Jana’izar Mahaifin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kogi, Alh. Ahmed Momoh Sani Ododo, a garin Okene dake jihar Kano, ayau Talata.
Muna roƙon Allah S.W.T cikin Rahamar Sa da Jinƙan Sa, Ya Gafarta masa, Ya sada shi da Aljannar Firdausi. Ya kuma bawa dukkan Ahalin Ahmed Sani Ododo haƙurin jure wannan babban rashi.
Abubakar Musa DK
Media Aide to H.E Dr. Nasiru Yusuf Gawuna
19/August/2025.

