

Bunkure Ta Jaddada Muhimmancin Hada Mata a Tattalin Arziki a UNGA80
Karamar Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Dakta Mariya Mahmoud Bunkure, ta bayyana cewa karfafa tattalin arzikin mata hanya ce mai inganci wajen rage talauci, samar da daidaito da kuma wanzar da zaman lafiya mai dorewa.
Ta bayyana hakan ne a birnin New York, yayin wani taron musamman da aka shirya kan karfafa tattalin arzikin mata, inda shugabannin siyasa mata da masana tattalin arziki suka halarta, a yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 (UNGA80).
Dakta Bunkure ta jaddada cewa, karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shirin Renewed Hope Agenda ya mai da hankali wajen inganta damar mata a cikin gwamnati, raya matasa, tare da samar da sabbin hanyoyi da za su ba mata damar bunkasa a matsayin masu kirkire-kirkire, ‘yan kasuwa da kuma shugabanni.
Ta kuma tabbatar da cewa gwamnatin FCT na da niyyar ci gaba da samar da yanayi mai sauki da zai bai wa mata damar samun kudin jari, koyon kwarewa da shiga harkokin kasuwanci, domin su taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa.
Ministar ta yaba wa masu shirya taron, inda ta ce wannan dandali muhimmin fili ne da ake hada manufofi da dabaru domin hanzarta cigaban duniya a fannin karfafa mata.
A cewar ta, baiwa mata cikakken ‘yancin tattalin arziki ba wai kawai ginshikin ci gaban kasa ba ne, har ila yau yana da matukar muhimmanci wajen gina al’umma mai adalci da zaman lafiya mai dorewa.

