
DR.. BAFFA BABBA DAN’AGUNDI YA BAYAR DA TALLAFIN NAIRA MILIYAN 4,500,000 GA YAN KUNGIYOYI AKAN MATSALOLIN DABAN DABAN
Jagora Hon. Baffa Babba Dan’agundi, NIM, DG NPC, ya ci gaba da cika alƙawarinsa na tallafawa mambobin ƙungiyoyi kamar yadda ya alqawarta tun a farkon tafiyar kungiyoyi.
A wannan makon ma, ya amince da biyan tallafin kuɗaɗe da suka kai kimanin Naira Miliyan (₦4,500,000) ga mutane daban-daban, wanda ya haɗa da tallafin rashin lafiya, ibtila’in gobara, tallafin karatu da na aure.
Wannan na daga cikin ayyukan alkhairi da Jagora ke yi domin taimakon al’umma musamman yayan kungiyoyi domin rage raɗaɗin rayuwa.
Allah Ya saka masa da alkhairi, Ya biya masa dukkan buƙatunsa.
Hon. Nasiru Usman Naibawa (Zico)
SLA ga Shugaban Majalisar Dattijai
11-06-2026

