
AYUBA JARUMI
Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta NPC
Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi
ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar AOC Youth Ambassadors na kasa a ofishinsa dake birnin tarayya Abuja, inda suka tattauna muhimman abubuwan da suka shafi cigaban matasa da kuma Jam’iyyar mu ta APC musamman a kakar zabe ta shekarar 2027. A nasa bangaren Babban Daraktan ya nuna farin cikinsa da wannan zayarar inda ya sha alwashin ci gaba da bayar da tallafinsa a kowane fanni domin cigaba da samun Nasarar Jamiyyar APC a matakin jahohi, kananan hukumomi da mazabu da kuma kasa baki daya.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08038124374 ko abknaisa100@yahoo.com

