
Dalilin da Ya Sa Murtala Sule Garo Ya Zama Jigon Siyasa Daga Tushe a Jihar Kano
Musaddiq Wada Waziri
A fagen siyasar Kano, inda a mafi yawan lokuta mutane ke tunanin cewa tasirin siyasa yana zuwa ne daga matsayi ko kusanci da masu mulki, Murtala Sule Garo, wanda aka fi sani da “Kwamanda,” ya bayyana kansa a matsayin ɗan siyasa da tasirin sa ya fito kai tsaye daga kyakkyawar alaƙar sa da al’umma. Ba wai masanin dabarun siyasa ba ne kaɗai, a’a, mutum ne da ko yaushe yake cikin huldar jama’a, wanda tasirin sa ba ya gushewa ko da lokacin da baya riƙe da wani muƙamin gwamnati.
Kwamanda yana da zurfin fahimtar yanayin siyasar Kano da kuma wani ilimi mai tushe a cikin al’ummar jihar, wanda hakan ya ba shi damar shiga zukatan jama’a ta wata hanya da ɗimbin sauran ‘yan siyasa ba za su iya amfani da ita ba. Shi ne gwarzon da ya fi kowa sanin yadda za a tafiyar da zukatan al’ummar Kano a wannan lokaci da muke ciki.
Abin da ya fi banbanta shi da sauran ‘yan siyasa shi ne, yana bayyana damuwarsa da kishi na gaskiya ga magoya baya da al’umma baki ɗaya. Salon siyasar Garo ya ta’allaka ne wajen shiga cikin rayuwar al’umma domin tallafa musu. A ko wanne yanayi yana kasancewa mai shiga cikin al’umma domin taya su murna ko baƙin cikin wani hali da suka tsinci kansu a ciki. A yau za a gan shi a bikin aure, gobe kuma za a iya samun sa a wajen jimami ga waɗanda suka rasa wani makusanci. Wannan nauyi da ya ɗauka wajen kasancewa tare da jama’a a lokutan farin ciki da bakin ciki ita ce ginshiƙin soyayya da biyayya da gaskiya da yake samu. Huldarsa da jama’a na daɗa tabbatar da irin jagorancin da ya gina a kan sadaukarwa da kasancewa a kusa da mutane.
Wata shaidar da ta fi bayyana irin kusancin sa da jama’a ita ce yadda gidan sa ke cikar kwari a duk lokacin da ya shigo jihar Kano. Harabar gidan sa na zama tamkar cibiyar siyasa da taron jama’a, ko kuma wani filin da al’umma ke amfani da shi domin ziyara da sada zumunta. An san shi a matsayin ɗan siyasa jajirtacce a jihar Kano da kullum yake buɗe kofar sa ga jama’a cikin adadi mai tarin yawa. Sau da yawa fiye da mutum dubu guda kan ziyarci gidan sa a rana ɗaya, daga kowane yanki na Kano har ma daga makwabtan jihohi, domin su gaisa da shi, su tattauna da shi a kan matsalolin su, ko neman shawara. Wannan halayyar ba wai al’ada ce kawai ba, a’a, wani yanayin alƙawari ne na kasancewa cikin jama’a da ya zama masa yanayi mai tasiri da samun wajen zama a zukatan mutane.
Tasirin siyasar Garo ya ta’allaka ne a kan gaskiya, juriya, da rikon amana. A lokacin da siyasa ta cika da alkawuran da basu da muhimmanci, Kwamanda yana tafiyar da al’amuran sa cikin natsuwa. Baza ka same shi yayi magana ko alƙawarin da ba zai iya cikawa ba, kalaman sa suna da girma saboda yana tabbatar da su a aikace. Sunan sa a matsayin gogagge kuma gwarzon ɗan siyasa ya tabbata a gare shi ba tare da shakka ko kokwanto ba. Baya jin tsoro ko ja da baya wajen kare mutuncin magoya bayan sa da al’ummar da suka yarda da jagorancin sa. Wannan jajircewa tare da karamci da goyon bayan da yake bawa matasa da sauran jama’a musamman a cikin tafiyar jam’iyyar APC, shi ne ya bayyana dalilin da ya sa magoya bayan sa ke yin tsayin daka a kan duk wani lamarin sa. Ko a yanzu da baya riƙe da wani muƙami, tasirin sa da taimakon da yake yi wa jama’a ya fi na masu riƙe muƙamin gwamnati a yau.
Ɗorewar tasirin Murtala Sule Garo a siyasar Kano ta yau, babban darasi ne ga masu yin siyasa da neman matsayi, hakan ya tabbatar da cewa a jihar Kano, ba a yin amfani da kujera ko wani choge wajen ƙarfafa tasirin mutum, sai dai a yi hakan ta hanyar duba yawan ƙofofin da yake buɗewa don cigaban al’umma da kuma yawan mutanen da ya tallafawa da hannunsa ba lokacin bukata ba

