
DA DUMI-DUMI: Kotu ta samu Nnamdi Kanu da laifi kan tuhumar ta’addanci da Gwamnatin Tarayya ta yi masa
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu jagoran ƙungiyar IPOB da ke tsare, Nnamdi Kanu, da laifi a kan tuhumar farko daga cikin tuhumomin ta’addanci da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a kansa.
A hukuncinta, kotun ta ce ta gamsu cewa Kanu ya yi jerin bayanai ta kafafen watsa labarai da nufin tayar da tarzoma da kisa, a cikin yunƙurin neman ballewar Biafra.
Yayin karanta hukuncin, Mai Shari’a James Omotosho ya ce ya dogara ne kan “shaida da ba a ƙalubalanta ba” da masu gabatar da ƙara suka gabatar, wadda bangaren kariya bai iya karyatawa ba.

