
Sama Da Shekaru 45 Dharmendra Ya Musuluntà Ta Dalilin Auren Abokiyar Aikinsa, Hema Malini
An haifi Dharmendra a cikin iyalin Punjabi Jat waɗanda ke bin addinin Hindu Arya Samaj. Daga baya ya koma Musulunci a ranar 21 ga Agusta, 1979, saboda ya samu damar auren Hema Malini, inda ya canza sunansa zuwa Dilawar Khan a lokacin. Saboda addininsu na Hindu bai ba shi damar auren mace fiye da daya ba.
Hakan ya ba shi damar auren Hema Malini bisa doka yayin da matarsa ta farko ke raye har yanzu, saboda ba bisa doka ba ne ga namijin Hindu ya sake yin aure a ƙarƙashin dokar auren Hindu.
Tun daga lokacin Dharmendra ya ci gaba da yin addinin Musulunci har zuwa rasuwarsa a yau.
Mun samu tarihin hakan ne a shafin Google

