
APC Ta Nemi ’Yan Takara Su Yi Sulhu A Kano
Jiga-jigan Jam’iyyar APC a Jihar Kano sun yi kira da a fitar da ’yan takara ta hanyar sasanci kafin babban zaɓe mai zuwa, a matsayin mataki na ƙarfafa haɗin kan jam’iyya da kauce wa rikice-rikicen cikin gida.
An yi wannan kira ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano da yammacin Alhamis.
A jawabinsa ga ’yan jam’iyya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana taron a matsayin mai cike da tarihi, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai da sabon salo na siyasa a jihar.
Gwamna Abba ya buƙaci ’yan jam’iyya su rungumi tsarin sasanci wajen fitar da ’yan takara maimakon yin zaɓen fidda gwani.
Ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyya sun samu umarni da su tabbatar da an kammala sasanci a matakin jiha domin sauƙaƙa tsari, inda ya nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamna Abba ya kuma buƙaci masu neman takara da su yi sasanci a mazaɓunsu, yana mai jaddada cewa haɗin kan cikin gida shi ne mabuɗin nasarar jam’iyya.

