
Masarautar Ningi Ta Nada Bichi Matsayin Sa’in Tudun Wada Galala
Masarautar Ningi karkashin Sarkin Tudun WADA dake karamar hukumar Wardi ta jahar Bauchi Alhaji Kamis Ahmad ta gabatar da takardar sarautar Sa’in Tudun Wada Galala ga shugaban hukumar gudanarwar ta raya kogunan Hadeja Jama’are, Inginiya Rabiu Suleiman Bichi a ofishin hukumar dake Hotoro, Kano.
Da yake jawabi yayin mika takardar sarautar, Sarkin na Tudun wada A. Kamis Ahmad yace masarautar tayi wannan abunne dan gane da yadda shugaban hukumar gudanarwar ta raya kogunan Hadeja Jama’are yake gudanar da aiyukansa da kuma jajircewarsa, gaskiya da rikon amana wajan ganin harkar noma ta samu kulawa da bunkasa.
“Yau munzune domin mika takardar shedar zama Sa’in Tudun wada Galala ga mai girma shugaban hukumar Hadeja Jama’are Inginiya Rabiu Suleiman Bichi a matsayin Sa’in Tudun wada Galala dan irin kokarin da yake wajan bunkasa harkar noma a wannan yankin namu. Tunda muke ba wani MD da ya taba zuwa Galala dan yaga irin halin da muke ciki. Amman zuwan Inginiya Rabiu Suleiman Bichi yaje kafa da kafa yaga halin da muke ciki kuma yayi mana abubuwa da dama. Hakan yasa muka dacewarsa muzu mu mika masa wannan shedar tare da wasu kyaututtuka domin kara masa kwarin gwaiwa.
Ya kuma taya sabon Sa’in murnar wannan sarautar da fatan zai kara jajircewa akan ayyukan da yake gudanarwa domin cigaban harkar noma.
Anasa bayanin yayin karbar takardar kama aiki a matsayin sabon Sa’in na Tudun wada Galala, Inginiya Rabiu Suleiman Bichi nuna farin cikinsu yayi bisa wannan abun alkhairi. A cewarsa ” wannan babbar ranace domin itace ta farko a wajena da masarauta taga ya dace a nadani a wani matsayi na sarauta”
Ya kuma godewa sarkin na Tudun wada Galala da masarautar ta Tudun wada bisa wannan matsayi da akaga dacewarsa dan bada tasa irin gudun mawar dan cigaban yanki. A kashe yayi addu’ar Allah ya mayar da kuwa gidansa lafiya.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 08027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

