
Mataimakin shugaban jami’ar Skyline Farfesa Ajith Kumar V.V ya bukaci mahalarta taron bita na kwana daya da jami’ar ta shirya don amfani da fasahar da ta dace don shiga cikin kalubalen duniya.
Mataimakin shugaban jami’ar ya tattauna hakan ne a wajen bude taron bitar da aka gudanar a harabar jami’ar.
Farfesa Ajith Kumar ya nuna bukatar mahalarta taron su yi amfani da dabarun da suka yi amfani da kungiyarsu.
Mahalarta taron bitar daga Guarantee Radio da sauran kafafan yada labarai daban daban a jihar Kano sun halarci taron bitar.
Wakilinmu a cikin bitar Abdullahi Adamu Dirimin ‘iya R ya ruwaito cewa Mataimakin shugaban jami’ar ya ce, an shirya taron ne a matsayin wani bangare na ayyukan zamantakewa na jami’ar.
Farfesa Ajith ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya da kyau.
Babban manajan gidan rediyon Guarantee Alhaji Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya jagoranci mahalarta dabarun jagoranci da fasaha masu mahimmanci.

