
An cafke jami’an sojan ruwa na bogi a Lagos
Hukumar kare muhalli da aikata laifuka na musamman ta Jihar Lagos ta cafke mutane uku bisa zargin zama jami’an sojan ruwa na bogi domin damfarar mazauna yankin da kuma hana aiwatar da halaltattun ayyukan gwamnati.
Kakakin hukumar, Abdulraheem Gbadeyan ne, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Lagos.
Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne yayin wani aikin tabbatar da doka bayan rushe rumfunan da aka yi ba bisa ka’ida ba da kuma mamaye filayen gwamnati a yankin Oworonshoki.
“Waɗannan masu sojan gonar sun rika bayyana kansu a matsayin jami’an sojan ruwa domin tsoratar da mazauna yankin, kauce wa matakan aiwatar da doka, yayin ayyukan gwamnati,” in ji Gbadeyan.
Ya ƙara da cewa babban wanda ake zargin ya je hedikwatar hukumar yana neman a saki motocin da aka kwashe daga wajen da aka rushe.

