Wata kungiya mai Rajin kare Mutuncin Kano tayi kira ga Gwamnati data dawo da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero kan karagar sarautar jihar.
Shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Abubakar Chiroma shine ya bukaci hakan a wata ganawa da yayi da manema Labarai a birnin Kano.
Alhaji Abubakar Chiroma yace tunda dai yanzu Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu “yancin kansa ya zama tabbataccen mai cikakken iko to ya kamata ya dawowa da al’umar Kano Sarkin da suke so.
Kamar yadda yace a jawabinsa a ranar da yake dawowa cikin Jam’iyar APC “Yanzu mu ba makafi bane idon mu ya bude munga haske” to ya kamata Gwamnan yayi gaggawar warware matsalar masaratar jihar ya tabbatar da Sarkin Kano a Matsayin Sarkin da al’umar Kano suke so kuma suke kauna.
Shugaban Kungiyar ta masu kare Mutuncin Kano yace ada ana zargin wasu abubuwa da suke faruwa ana tilastawa Gwamnan ne to amma yanzu tunda sun raba hanya ta siyasa da jagoransa ya kamata ya mayar da hankali wajan cigaban kano da alumar jihar kamar yadda yake fada a jawabansa.
Kungiyar daga nan sai ta yabawa Gwamnan bisa saka son jihar kano da alumar jihar a gaba fiye da bukatun kansa da na wani, wannan babban abun yabawa ne a gareshi.
Daga nan kungiyar ta jaddada bukatar alumar jihar kano su cigaba dabin doka da oda, tareda kaunar son zaman lafiya da karuwar arziki a jihar da kasa baki daya.

