
Shugaban Hukumar kula da aikin Hajjin na Kasa Farfesa Abdullahi Sale Pakistan yayi wannan bayani ne lokacin da yake karbar bakuncin wata Kungiyar cigaban Matasa.
Kungiyar ta ziyarci Farfesan ne domin Karrama shi bisa irin yadda yake jajircewa da gudanar da ayyukansa domin cigaban al’uma.
Shugaban Hukumar kula da aikin Hajjin na Kasa Farfesa sale Pakistan yace yaki dadin yadda yaga Kungiyar ta hada Kan Matasa Kuma masu ra’ayin siyasa daban daban Yana Mai cewa wannan wani babban cigaba ne.
Yace a bangaren neman ilimin da yayi, yayi bincike tare da gano cewa addinin Musulunci ya Samar da hanyoyin magance Talauci da yawan gaske.
A don haka ne ya bukaci Matasan su Dunga kokarin samawa Matasa ayyukan yi a tsakaninsu domin rage yawan Matasa Matasa ayyukan yi a tsakanin Al’uma.
Yace a nasa bangaren zai taimakawa Kungiyar domin samun sukunin cigabansu da Kuma gudanar da ayyukansu tareda taimakon matsala da sauran Al’uma.
Pakistan yayi musu addu’ar Allah ya cigaba da basu karfin guiwar cigaba da wayar da Kan sauran yan uwansu Matasa domin samun nasarar abubuwan da suka sa a gaba

