
Abba Kaɗai Ke Da Takarar Kai-Tsaye A Kano —APC
Jam’iyyar APC ta saya wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na fom ɗin neman tazarce babu hamayya a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Shugabannin Jam’iyyar APC sun ɗauki wannan mataki ne bayan sun rungumi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba a matsayin ’yan takara babu hamayya a kujerar shugaban ƙasa da na Gwamnan Jihar Kano a zaɓen na 2027.
APC ta amince da takarar Tinubu da Abba babu hamayya ne bayan Rabiu Suleiman Bichi ya gabatar da ƙudurin a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kano a ranar Alhamis.
Tsohon Gwamnan Jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da haka, tare da miƙa wa Gwamna Abba fon din takarar neman wa’adi na biyu da jam’iyyar ta saya masa.
Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC Reshen Jihar Kano ba ta amince da bayar da tikitin takarar kai-tsaye ga masu neman sauran kujeru ba a zaɓen 2027.
Ya bayyana cewa a maimakon haka, APC ta amince a yi sulhu tsakanin masu neman takara domin tabbatar da adalci da kawar da ruɗani a cikin jam’iyyar.

