
Faruwar Haddura ya Ta’azzara yayin da kusan Kullum sai an rasa Rayuka Sakamakon aron hannu akan Hanyar Karfi – Kura a Titin Zaria.
Duk da irin Kokarin Gwamnati na kula da Kuma tsare rayukan Al’uma a bangarori daban daban, Amma abun yaci tura a hanyar karfi zuwa kura akan titin Zaria dake Kano.
Matuka ababan hawa Kama daga Kananan zuwa manyan Motoci dake aron hannu a wadannan hanyoyi da muka zayyana kan samu kansu cikin mummunan yanayi inda wasu ma ke rasa Ransu.
Kamar yadda Jaridar Abknews24 ta zanta da wani Wanda kebin hanyar a Kullum Alhaji Hamza Kura yace babu wata rana da za’a wayi gari da ba’ayi hatsari a wannan hanya ba.
Hamza yace Tun Ana iya kokarin magance matsalar Amma yanzu abun yaci tura Kuma ga dukkan alamun lamarin yafi karfin jami’an dake kula da kiyaye Haddura na FRSC dana KAROTA.
Hamza Kura ya kara da cewa Koda a ranar Alhamis da juma’a da Asabar 13/06/2026 sai da irin wannan Mummunan Hatsari ya faru a wannan hanya.
Yace a Kullum Asibitin garin Kura sai ya karbi mutanen da suka samu raunuka da Kuma gwarwakin Al’uma.
A don haka ne Al’umar yankin ke kira ga mahukunta dasu dauki Matakin gaggawa domin ceto rayukan Al’uma da sauran matafiya dake bin wannan hanya.

