
Gwamnatin jihar Kogi ta rufe kasuwanni da tashoshin mota saboda matsalar tsaro
Gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da rufe wasu kasuwanni da tashoshin mota na ɗan lokaci a sassan Yankin Kogi ta Yamma, a wani mataki na ƙara tsaurara matakan tsaro domin fatattakar ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Mista Kingsley Fanwo, ya fitar a yau 8 ga watan Fabrairun shekarar 2026
Fanwo ya ce rufe kasuwannin da tashoshin motar na daga cikin goyon bayan da gwamnatin jihar ke bai wa ayyukan samar da tsaro da ake gudanarwa, tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro da kuma shugabannin hukumomin tsaro a jihar Kogi.

