Daga Abba Anwar:

Gamayyar kungiyoyin ƙasashen yankin Sahel ta ƙarƙashin Réseau des Jeunes du Sahel pour le Progrès, le Développement et la Démocratie (RJS-PDD) ta karrama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin, saboda rawar da yake takawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da haɗin kan Afirka.
A wani taron karramawa da aka gudanar a birnin Abuja, shugaban gamayyar, Mista Fassoko Doumbia, wanda Dr. Najib Usman ya wakilta, ya bayyana cewa an zabi Sanata Barau daga cikin fitattun ‘yan takara guda shida daga ƙasashen yankin don lashe wannan kyauta ta farko wacce aka fi sani da Sankofa Award for Legislative Excellence in Africa.
“Sanata Barau mutum ne da ya nuna kishin ƙasa da kishin Afirka baki ɗaya. A matsayinsa na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da kuma Mataimakin Kakakin Majalisar ECOWAS, ya taka rawa wajen samar da ci gaba mai ɗorewa ta fuskar ilimi, ƙarfafa samar da ababen more rayuwa da haɗa kan jama’a,” in ji shi.
Masu gabatar da kyautar sun bayyana cewa wannan lambar yabo ta nuna irin tasirin jagoranci da jajircewar Sanata Barau wajen sauya ma’anar aikin majalisa daga doka kawai zuwa gina al’umma da kuma samar da haɗin kai.
A jawabinsa bayan karɓar lambar girmamawar, Sanata Barau ya nuna farin cikinsa, inda ya ce “Ina matuƙar godiya da wannan girmamawa. Amma ina daukar wannan ba a matsayin nasara ta ƙarshe ba, illa kira ne gare ni da in ƙara jajircewa wajen hidimar ƙasata da yankinmu.”
Sanata Barau ya kuma yi kira da a dawo da ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar cikin ƙungiyar ECOWAS, yana mai cewa:
“Idan aka dubi tarihinmu da tsarin zamantakewarmu, muna da alaƙa ɗaya. Don haka ya kamata mu ci gaba da haɗa kai domin samun cigaba da zaman lafiya.”
A cikin jawabansa, Dr. Usman ya yi kira ga shugabannin ƙasashen yammacin Afirka da su ɗauki matakan haɗin kai, yana mai cewa:
“Kalubalen da muke fuskanta na tsaro, talauci da rashin daidaito ba za a magance su da rabuwar kai ba. Lokaci ya yi da za mu gina sabuwar hanya ta haɗin kai da zaman lafiya.”
Kyautar Sankofa Award ta kasance irinta ta farko a tarihin ƙungiyar, abin da ke nuni da yadda aka yaba da gagarumin rawar da Sanata Barau Jibrin ke takawa wajen kyautata shugabanci da ci gaban yankin.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar 07027324462 ko a abknaisa100@yahoo.com

