
Ɗalibi dan aji uku ya rataye kansa a Jami’ar jihar Neja
Wani ɗalibi dake aji na 3 a sashen Kimiyyar na’ura( computer science ) a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai, jihar Neja, mai suna Kelvin Danlami, ana zargin ya kashe kansa bayan ya yi asarar Naira 600,000 ta hanyar yin caca.
Majiyoyi sun bayyana cewa an ba marigayin ajiyar kuɗinwani aiki, amma sai ya yi amfani da kuɗin wajen caca.
Wani makwabcin ɗalibin ne ya gano gawar marigayin rataye a rufin ɗakinsa wanda daga nan ya sanar da hukumomi.
Ɗaya daga cikin ɗaliban jami’ar, wanda ya yi magana da jaridar Daily Trust, ya ce:
“Gaskiya ne ɗaya daga cikin abokan karatunmu ya kashe kansa bayan ya batar da kuɗin da aka ba shi amanar biyan kuɗin haya sakamakon yin caca.”
Mai magana da yawun rundunar ’yansandan jihar Niger, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust.

