
Ƙaramar Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta gwangawaje abokan aikinta na Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da kaɓakin arziƙi, inda ta rabawa wasu miliyan ɗaya-ɗaya, wasu dubu dari biyar, wasu dubu dari biyu da hamsin, wasu dubu dari, wasu kuma dubu hamsin — kowannensu.
Da yake jawabi yayin bada kaɓakin arziƙin, Dr. Idris Ado Muhammad (Adebo), wanda shi ya wakilci Ƙaramar Ministar Abujan wajen miƙa saƙon tallafin, ya ce wannan yana cikin ƙudure-ƙuduren ta na cigaba da tallafawa ma’aikatan da ke tare da ita da sauran al’umma.
Ya ƙara da cewa batun cigaba da tallafawa abokan aikin nata na Asibitin yanzu ne aka fara, za’a cigaba da yi lokaci zuwa lokaci dan tallafawa sauran ma’aikatan.
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Asibitin Koyarwar Malam Aminu Kano (AKTH) CMD, Prof. Abdurrahman Abba Sheshe, ya ce abubuwan da take musu ba za su ƙidayu ba, sai dai su roƙa Allah Ya saka mata da mafi girman alkhairi Ya kuma ƙara ɗaukaka matsayinta.
Ya ce cikin ma’aikatan da suke aiki tare, bayan waɗanda ta basu kaɓakan alkhairi irin wannan, akwai masu yawa da ta biyawa kujerar Makka — domin a 2024 da ya je Makka ya ga ma’aikatan sa da dama da ita ta biya musu. Har ma da patient ɗinta tana taimakawa har yanzu. Haka kuma a halin yanzu ta saka kuɗi domin a faɗaɗa sashen Family Medicine na AKTH. Saboda haka ake cewa ‘naka sai naka’. Muna fatan Allah Ya cigaba da yi mata jagora.

